Ranar Talata 19 ga wata, kakakin MDD Steaphane Dujarric ya ce, adadin wadanda suka kamu da cutar Ebola a kasashen Guinea, Liberia, Nigeria da Saliyo sun kai 2,240, kuma adadin wadanda suka mutu sun kai 1,229.
Dujarric wanda ya yi amfani da bayanan da suka fito daga hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO dangane da cutar ta Ebola ya ce, hukumar WHO tana aiki tare da hukumar tsara shiri kan samar da abinci ta kasa da kasa wato WFP domin tabbatar da ganin mutanen da aka kebe saboda cutar ta Ebola suna samun abinci a ko wane lokaci da kuma wasu ababen bukatu.
Kakakin MDD ya kara da cewa, tuni aka aika wa majiyyata abinci, wadanda aka kebe a asibitoci ko a gidajensu.
Gwamnatocin yammacin Afirka sun kafa wuraren kebe jama'a a wuraren da cutar ta yi kamarin gaske kamar Gueckedou a Guinea, Kenema da Kailahun a Saliyo da kuma Foya a Liberia. (Suwaiba)