Gwamnatin Najeriya ta sanar a ranar Litinin cewa, ta dakatar har zuwa yanzu matakinta kan amincewa da wani maganin yaki da cutar Ebola, Nano-Silver, da wani dan kasarta ya sarrafa. Ministan kiwon lafiyar kasar Onyebuchi Chukwu ya yi wannan sanarwa a birnin Abuja, a yayin da yake ganawa da jakadan kasar Amurka dake Najeriya, mista James Entwistle.
Maganin Nano-Silver, da aka baiwa cibiyar gudanar da ayyukan gaggawa dake Lagos a ranar 14 ga watan Augusta, ba ya amsa wasu muhimman sharuda na bincike ba, in ji mista Chukwu. (Maman Ada)