Babban sakataren zartaswa na kungiyar ci-gaban gabashin Afrika SADC, Stergomena Lawrence Tax, ta bayyana a ranar Litinin cewa kasashe mambobin goma sha biyar na gamayyar SADC ba za su amince da hana tafiya ba bisa dalilin cewa wasu daga kasashen yammacin Afrika suna fama da cutar Ebola.
Kungiyar SADC ba za ta hana masu tafiya ba kana ba za ta takaita zirga-zirgar jiragen sama dake fitowa daga kasashen da cutar ta shafa ba, in ji madam Tax a cikin wata hirarta tare da kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua a yayin dandalin shugabannin kasashe da gwamnatocin kungiyar SADC karo na 34. (Maman Ada)