in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhu na MDD ya bukaci a tallafi aikin binciken hadarin jirgin sama na MH17
2014-07-22 10:44:28 cri

Kwamitin sulhu na MDD ya zartas da wani kuduri, dake matukar nuna takaici game da faduwar jirgin saman nan na kasar Malaysia mai lamba MH17, a sa'i daya kuma ya kalubalanci bangarori daban daban da batun ya shafa, da su samar da taimako ga aikin bin bahasin musabbabin aukuwar hadarin, wanda tawagar kasa da kasa ke gudanarwa.

Kwamitin sulhun wanda ya tsayar da wannan kuduri a jiya Litinin 21 ga wata, ya kuma bayyana goyon bayansa ga aikin binciken wannan hadari, wanda tawagar kasa da kasa ke gudanarwa cikin 'yanci daga dukkan fannoni, bisa kuma ka'idojin jiragen saman fasinja na kasa da kasa.

Haka zakila ya bukaci dakarun da ke iko da wurin da wannan jirgin saman ya fadi, da kuma sauran yankunan da ke kewayensa da su kauracewa daukar dukkanin wani mataki na batar da shaidu, su kuma amince masu bincike su shiga yankin lami lafiya ba tare da wani tarnaki ba.

A nasa tsokaci kuwa zaunannen wakilin kasar Sin da ke MDD Liu Jieyi, ya bayyana cewa, kasar Sin na goyon bayan aikin binciken musabbabin faduwar jirgin saman na MH17 cikin 'yanci da adalci. Ya ce ya kamata kungiyar jiragen saman fasinja ta kasa da kasa, ta taka muhimmiyar rawa wajen binciken hadarin, a matsayinta na hukumar musamman ta MDD dake daidaita batutuwa masu alaka da jiragen saman fasinja.

Bugu da kari kuma, shi ma ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana gamsuwa da kudurin da kwamitin sulhun majalissar ya zartas kan lamarin, yana mai cewa, abin da ya fi dacewa a gaggauta aiwatarwa a yanzu shi ne aiwatar da wannan kudurin yadda ya kamata, musamman ma ta fuskar amincewa da masu bincike na kasa da kasa su shiga wurin da jirgin ya fadi domin gudanar da aiki. Ban da wannan kuma, ya jaddada cewa, kamata ya yi a kauracewa duk wani zato maras tushe, ko fidda wata sanarwa mai alaka da siyasa, gabanin kammalar aikin binciken.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China