in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron hukumomin kasa da kasa da na AU ya yi kiran da dauki matakan yaki da cutar Ebola
2014-08-19 10:14:31 cri

A ranar Litinin ne aka kira wani taro a hedkwatar kungiyar Tarayyar Afirka wato AU da nufin musayar bayanai kan yadda za a yi yaki da cutar nan ta Ebola mai saurin halaka jama'a.

Hukumomin kasa da kasa da na AU ne suka shirya taron da nufin samar da muhimman bayanai da matakan da kwararrun lafiya ke dauka, nasarorin da aka samu da kuma kalubalen da ake fuskanta tun lokacin da cutar ta barke, kana daga bisani a yi musayar kayan aiki da kwarewa ta yadda za a tunkari matsalolin da suka shafi lafiya a kasashen Afirka.

Kwamishinan kula da harkokin jin dadin jama'a na AU Olawale Maiyegun, ya bayyana bukatar da ke akwai ta hada karfi don magance matsalar. Haka kuma jami'an diflomasiya na kasashen da wannan cuta ta shafa, sun yi karin haske da kuma matakan da ake dauka kan cutar, yayin da wasu suka bayyana kudurinsu na bayar da goyon baya kan yadda za a tunkari wannan cuta.

Ya zuwa yanzu dai cutar ta Ebola wadda ta yadu a kasashen Liberia, Saliyo da Najeriya ta halaka sama da mutane 1,000 ciki hadda ma'aikatan lafiya tun bullarta a watan Maris.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China