in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wata 'yar Nijeriya da ta yada zango Hadaddiyar Daular Larabawa ta nuna alamun kamuwa da cutar Ebola
2014-08-18 11:14:27 cri
Wata mace mai kimani shekaru talatin da biyar 'yar Nigeria, wacce ke kan hanyar ta zuwa wani asibiti a India, saboda ciwon kansa, ta rasu a hadaddiyar daular larabawa inda ta yada zango, bayan da ta nuna alamun kamuwa da cutar Ebola mai saurin kashe bil'adama.

Kamfanin dillancin labarai na Hadaddiyar daular larabawa-WAM ya ce hukumomin lafiya na Abu Dhabi, sun ce a yayin da matar ta yada zango a filin saukar jiragen kasashen waje na Abu-Dhabi, sai ciwon nata ya tabarbare nan take, duk da kasancewar hukumomin lafiya na kasar sun ba ta kulawar da ta dace, to amma sai aka kasa farfado da ita, kuma matar ta nuna alamun yiwuwar kamuwa da cutar Ebola.

Sanarwar Hukumar lafiyar ta Abu Dhabi, tace sun rigaya sun dauki matakan da ya dace na kare lafiyar jami'an lafiya da suka duba lafiyar matar, kamar dai yadda ka'idojin hukumar lafiya ta duniya-WHO, suka tanada domin murkushe cuta mai saurin yaduwa.

Hakazalika hukumar lafiya ta Abhu Dhabi, ta kebe mijin 'yar Nigeriyar da kuma wasu jami'an kiwon lafiya guda biyar wadanda suka duba lafiyar matar, har sai bayan an samu sakamakon gwajin da aka yiwa matar, kuma kawo ya zuwa yanzu wadanda suka yi hulda da ita basu nuna wasu alamu na kamuwa da cutar ta Ebola ba. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China