Mamaciyar da ba'a bayyana sunanta ba, ta rasu a ranar Talata da yamma a wani asibitin dake Lagos, birni mafi yawan jama'a a Najeriya kuma hedkwatar tattalin arzikin kasar, in ji mista Chukwu a gaban 'yan jarida a birnin Abuja tare da bayyana cewa jami'ar kiwon lafiya ta yi mu'amala tare da Patrick Sawyer, wani dan Liberiya da ya mutu dalilin cutar Ebola yau da kusan makonni biyu da suka wuce.
Ba mu sani ba ko ita wannan jami'a tana daga cikin mutane takwas da ake zaton suna dauke da cutar Ebola a jihar Lagos.
Hukumomin kiwon lafiya sun bayyana cewa dukkan wadannan mutane da ake zaton sun kamu da cutar sun yi mu'amala tare da mista Sawyer.
A yayin wani taron manema labarai a ranar Talata, kwamishinan kiwon lafiya na Lagos, Jide Idris ya bayyana cewa an kebance wasu mutane shida ko da yake ba su da wata alama ta wannan cuta.
Hukumomin jihar suna ci gaba da kara kokarin neman duk mutanen da suka yi mu'amala da Sawyer, in ji mista Idris. (Maman Ada)