Guinea, Liberiya da Sierra Leone, kasashen da cutar Ebola ta fi shafa, tare da kasar Cote d'Ivoire za su gudanar da wani taron gaggawa a ranar yau Jumma'a a birnin Conakry, hedkwatar kasar Guinea, a cewar wata majiya mai tushe.
A cewar cibiyar watsa labarai ta fadar shugaban kasar Guinea, shugabannin kasashen Sierra Leone, Liberiya da Cote d'Ivoire ko kuma wakilansu za su halarci wannan taro.
Wannan muhimmin taro na shiyya ya kasance cigaban taron ministocin kiwon lafiya na Mano River Union a birnin Conakry na ranar 20 ga watan Yuni, da kuma taron baya bayan nan na ministocin kiwon lafiya na kasashen yammacin Afrika goma sha daya a birnin Accra a ranakun 2 da 3 ga watan Yuli.
Kasashen Guinea, Liberiya, Sierra Leone da Cote d'Ivoire, mambobi ne na kungiyar Mano River Union.
Darektar kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO, madam Margaret Chan, wakilan kungiyar Medecins Sans Frontiers (MSF) da sauran kungiyoyin ba da tallafi na kasar Guinea za su halarci wannan babban taro.
A cewar wani jami'in kiwon lafiya na ma'aikatar Guinea, wannan haduwa na manufar bayyana niyyar shugabannin kasashen shiyyar kan kokarin da suke na hana yaduwar cutar Ebola. (Maman Ada)