in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Nigeria ta ayyana dokar ta-baci kan bullar cutar Ebola
2014-08-07 09:59:51 cri
Gwamnatin Nigeria ta bayyana barkewar cutar Ebola a matsayin shiga cikin shirin ko ta kwana.

Ministan lafiyar kasar Farfesa Onyebuchi Chuwu, ya bayyana hakan ne a lokacin wani taron gaggawa a kan bullar cutar Ebola wanda kwamitin lafiya, na majalisar dokokin kasar ya shirya a babban birnin kasar Abuja.

Ministan ya ce daga cikin 'yan Nigeria 6 wadandada suka kamu da cutar, daya ta mutu a ranar Talata, kana kuma sauran mutanen shidda suna ci gaba da shan magani da samun kulawa a asibiti.

Chukwu ya ce, halin da Nigeria ta shiga a sakamakon bullar cutar Ebola ya budewa duniya idanu a kan cewar kowane bil'adama a duniya na fuskantar barazanar barkewar cutar ta Ebola.

Hukumarlafiya ta duniya, WHO ta ce ya zuwa yanzu mutane fiye da dubu daya da dari bakwai suka kamu da cutar kuma daga cikin wannan adadin, mutane 932 tuni suka mutu a shekarar da muke ciki, daga kasashen Africa ta yamma wadanda suka hada da Guinea, Liberia, Nigeria da Saliyo. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China