Shugaban kasar Saliyo Ernest Bai Koroma ya kafa dokar gaggawa ta baci domin gwamnati ta samu damar yaki da cutar Ebola.
A cikin wata sanarwa da ya yi ta kafar yada labaran kasar a daren Laraba, shugaba Koroma ya kuma umurci kiyaye duk cibiyoyin kiwon lafiya dake lura da wadanda suka kamu da cutar don hana yaduwar ta.
Shugaban ya ce, 'yan sanda da sojoji za su ba da taimako ga ma'aikatan kiwon lafiya da kungiyoyi masu zaman kansu domin su gudanar da ayyukansu ba tare da wani cikas ba.
Haka kuma duk wani taron jama'a, an takaita shi sai dai kawai taron da ya zama wajibi da ya jibanci tattauna yadda za'a magance cutar Ebola, ko kuma ya jibanci batun wayar da kan jama'a da kara wa juna sani game da cutar. (Fatimah)