in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar zirga-zirgar jiragen saman Liberia ta dauki matakin murkushe Ebola
2014-07-30 10:46:39 cri

Hukumar zirga-zirgar jiragen sama ta Liberia ta bayyana cewar, za ta bi shawarwarin da ma'aikatar kiwon lafiya kasar ta gabatar a game da hana yaduwar kwayar cutar Ebola.

Hukumar kula da filin jirgin saman kasa da kasa na Roberts, RIA na kasar ta bayyana a cikin wata sanarwa cewar, za ta dauki wani mataki a game da mutanen dake shiga cikin jiragen, domin dakatar da yaduwar cutar Ebola, wadda har yanzu ba ta da magani.

Sanarwar ta ce, hukumar za ta ba da dama kawai ga fasinjoji wadanda ke da mallakin takardun bulaguro da doka ta amince da su, da kuma 'yan kasuwa da aka amince da su damar shiga jiragenta, kuma za ta ci gaba da daukar wannan matakin, har sai ma'aikatar lafiya ta kasar ta ba da sanarwar cewar, an murkushe cutar ta Ebola a Liberia.

Kawo ya zuwa yanzu, cutar ta Ebola ta haddasa asarar rayukan jama'a 129 a Liberia, kuma mutane kusan 700 ne suka rasa rayukansu a sakamakon cutar a kasashen Guinea, Liberia da Sierra leone, wadanda ke Afrika ta yamma. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China