in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afrika ta Kudu tana cikin shirin ko ta kwana a game da Ebola
2014-07-31 10:29:53 cri

Kasar Afrika ta Kudu ta daura damarar yaki da cutar Ebola a sakamakon barkewar cutar a Afrika ta yamma.

Ministan kiwon lafiya na Afrika ta Kudu Aaron Motsoaledi, ya fada a cikin wata sanarwa cewar, duk da yake kasar ta dauki wannan mataki, ya kamata jama'a su kau da fargaba a game da halin da ake ciki, domin ma'aikatar ta yi amanna a bisa cewar, tsauraran matakan da ta dauka na sa ido da yaki da cutar za su yi aiki.

Sanarwar ta ce, ma'aikatar lafiya ta rigaya ta yi bayani ga dukanin wadanda ya kamata a kan cutar ta Ebola mai saurin hallaka jama'a, wacce a halin yanzu ta shiga Afrika ta yamma.

Ma'aikatar ta ce, tuni ta sanya bangarori dake yaki da barkewar cuta cikin shirin ko ta kwana ko da za a samu alamun cutar a kasar, domin a murkushe lamarin nan take. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China