in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar direbobin Najeriya reshen jihar Yobe ta roki gwamnatin jihar da ta samar da na'urorin gano muggan makamai a tashoshin mota
2014-08-06 14:26:05 cri

Sakamakon yadda 'yan ta'adda suka fara canza salo wajen gudanar da ayyukansu na ta'addanci, kungiyar direbobi ta tarayyar Najeriya NURTW reshen jahar Yobe, ta roki gwamnatin jihar da ta samar musu na'urorin zamani, wadanda za a rika amfani da su don gano dukkannin wasu muggan makamai da aka iya boye su cikin motocin da 'ya'yan kungiyar ke amfani da su, wajen cutar da fasinjoji yayin tafiye-tafiye.

Wannan roko dai ya fito ne daga bakin shugaban kungiyar ta NURTW reshen jihar ta Yobe Alhaji Huseini Ibrahim, a tattauanwarsa da 'yan jaridu dangane da sabon salon ta'addanci da 'yan ta'addar suka fara bullo da shi, na tashin boma-bomai a wuraren taruwar jama'a, lamarin da kan haddasa rasa rayukan jama'a da dama.

Shugaban kungiyar ta NURTW ya ci gaba da cewa kungiyar tana daukar matakan gudanar da cikakken bincike kan kayayyakin da fasinjojin masu shiga tasha ke dauke da su, yayin tafiye-tafiye, don haka ya yi kira ga jama'a da su baiwa wannan aiki goyon baya, domin a samu nasarar kawar da barazanar da ake fuskanta daga bata garin da kan yi shigar burtu su na hallaka rayukan jama'a.

Alhaji Huseini Ibrahim ya ce, bai kama fasinjoji su dauki binciken kayan su a matsayin abin kunya ba, a cewarsa hakan shi ne zaman lafiya ga fasinjojin da kuma direbobin dake tuka motocin haya.

Shugaban kungiyar direbobin ya kuma roki mutanen dake barnata gadojin mota da su ji tsoron Allah su dakatar da wannan munanan aiki, kasancewar hakan na iya shafar kowa da kowa har da su ma kansu masu aikata wannan tabargaza.

Murtala, wakilin sashin Hausa na CRI, daga Abuja, Najeriya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China