in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Tarayyar Najeriya ya yi kira ga al'ummar kasar da su hada kai wajen yaki da Boko Haram
2014-07-17 15:58:05 cri
Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ya yi kira ga jama'ar kasar da su hada kai wajen yaki da kungiyar Boko Haram. Cikin wata sanarwa da fadar gwamnatin Najeriyar ta fitar a ranar 16 ga wata, an jaddada cewa tashe-tashen hankulan da kasar ke fuskanta a halin yanzu, sakamakon ayyukan kungiyar ta Boko Haram, na haifar da babbar matsala ga al'umma wajen cimma burikan su na rayuwa.

Sanarwar ta kuma jaddada bukatar ci gaba da daukar matakan yaki da kungiyar, ta yadda za a kai ga kawar da ita daga fadin kasar. Daga nan sai sanarwar ta godewa sauran kasashen duniya da ke nuna goyon baya, da taimakawa kasar a wannan aiki na dakile ayyukan kungiyar. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China