in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin Huawei ya zuba jarin kimanin dala dubu 500 a aikin horas da kwararru a Afrika
2014-07-20 17:32:24 cri

Kamfanin Huawei na kasar Sin, da hadin gwiwar cibiyar Nelson Mandela, sun kaddamar da shirin zuba jarin da yawan sa ya kai dala dubu 530, kudaden da za a yi amfani da su wajen gudanar da aikin horar da al'ummar nahiyar Afirka da dama ilimin kimiyya da fasaha.

A ya yin bikin kaddamar da shirin wanda ya gudana a jiya Asabar a birnin Abuja fadar gwamnatin Nijeria, an bayyana cewa za a yi amfani da kusan dala dubu 30 wajen samar da tallafin karatu ga jami'ar koyon ilmin kimiyya da fasaha ta nahiyar Afirka dake karkashen cibiyar, domin samawa masu bincike a fannin kimiyya da fasaha na wannan jami'a kudaden aiki.

Ban da haka kamfanin na Huawei ya baiwa kwalejin na'urorin sadarwa da darajansu ta kai dala dubu 500, domin taimakawa aikin kafa cibiyar nazarin kimiyya da fasaha. Lamarin da zai sanya kamfanin zama na farko da ya kafa irin wannan cibiya a Najeriya. Kaza lika Huawei zai bude cibiyar sa dake Abuja ga dalibai, domin karfafa musu gwiwar hada abubuwa da suka koya daga makaranta, da ayyuka da za su yi a wuraren aiki, duka da nufin karfafa kwarewar su wajen nazari, da hada kimiyya da aikin samar da kayayyaki wuri guda.

Mataimakin direkta na kamfanin Huawei dake Abuja Mr Yi Weize ya bayyana cewa, kawar da shingen kwarewa a fannin kimiyyar sadarwa na daya daga cikin muhimman kudurorin da kamfanin na Huawei ya sanya a gaba. Ya ce ya zuwa yanzu, Huawei ya kafa cibiyoyin horaswa a Afrika 7, kana ya na hadin gwiwa da jami'o'i fiye da 10 a fannin kimiyya da fasaha. A shekarar 2012 kamfanin na Huawei ya samar da tallafin karatu a fannin kimiyyar sadarwa a jami'ar Lagos dake Najeriya. Kana a shekarar 2013 kuma, ya kaddamar da shirin horar da duban 'yan mata injiniyoyi, sa'an nan a bana, ya kara habaka hadin gwiwarsa da kwalejin Nelson Mandela, wajen sanya ido kan samar da ilmi mai inganci, da horar da daliban kimiyya da fasaha, da zummar samar da karin kwararru a fannin fasahar sadarwa a Afrika. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China