in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar lafiya ta tarayyar Najeriya tana kokarin fadakar da jama'a game da cutar Ebola
2014-07-31 13:52:27 cri

A daidai gabar da masassarar Ebola mai saurin kisa ke ci gaba da yaduwa a wasu kasashen yammacin Afirka, kamar kasashen Guinea, da Laberiya, da Saliyo, hukumomin kiwon lafiya na tarayyar Najeriya na kokarin fadakar da jama'a kan wannan cuta.

Kwanan baya, cibiyar dakile yaduwar cututtuka da bada kariya ta Najeriya ko NCDC a takaice, da ma'aikatar lafiya ta kasar sun fitar da wata muhimmiyar sanarwar hadin gwiwa, dangane da kandagarkin yaduwar cutar ta Ebola. An kuma fitar da wannan sanarwa ne cikin harshen Turanci, gami da sauran manyan harsunan Najeriya guda uku, wato Hausa, da Yarabanci, da kuma Igbo.

Sanarwar ta ce, cutar Ebola mai saurin kisa, ana kamuwa da ita daga namun daji kamar jemagu, da birai irin su goggon biri. Kana bisa bayanan dake kunshe cikin sanarwa, alamomin kamuwa da cutar sun hada da zazzabi mai tsanani, da ciwon kai, da tari, da ciwon jiki da gabobi, da ciwon kirji da ciwon ciki. Sauran alamun sun hada da kasala, da gudanwa mai jini, da fitar jinni daga kunne, da ido da hanci, da kuma baki.

Har wa yau sanarwar ta yi nuni ga matakan kariya daga kamuwa da cutar ta Ebola, ciki har da tsaftace muhalli, da cin abinci ko nama da aka dafa sosai, musamman namun daji da makamantansu. Sa'an nan a kiyaye taba mutum ko dabba mai rai ko matacce wanda ya riga ya kamu da cutar, a kuma kiyaye taba jini, ko fitsari, ko yawu, ko bayan-gidan jemagu da birai.

A karshe sanarwa ta bayyana cewa, wannan cuta bata da magani, kuma ba ta da allurar rigakafi, don haka wajibi ne a hanzarta gabatar da rahoton duk wata alama, mai alaka da bullar cutar ga asibiti ko cibiyar lafiya dake kusa.

Sanarwar ta ce, domin neman karin bayani game da cutar Ebola, sai a tuntubi lambobin wayar ko-ta-kwana, wato 08037879701, 08037154575.

Murtala, wakilin sashin Hausa na CRI, daga Abuja, Najeriya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China