Kakakin ma'aikatar tsaron kasa ta tarayyar Nijeriya Chris Olukolade wanda ya bayar da wata sanarwa a wannan rana, ya ce, wani mutum mai suna Babuji Ya'ari ya jagoranci wannan gungun, wanda shi dan kasuwa ne mai sayar da motocin keke Napep wato mai tayoyi 3, kana shi memban kungiyar 'yan banga ne dake wurin. Ya'ari ya yi amfani da matsayinsa don gudanar da ayyukan leken asiri.
Janar Olukolade ya kara da cewa, tun daga shekarar 2011 zuwa yanzu, Ya'ari ya bada gudummawa wajen kai hare-hare a garin Maiduguri na jihar Borno dake arewa maso gabashin tarayyar Nijeriya. (Zainab)