in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An maida ba'amirken da ya kamu da cutar Ebola gida
2014-08-03 15:53:32 cri
Rahotannin daga kasar Amurka, na cewa an maida daya daga 'yan kasar biyu da suka kamu da cutar nan mai saurin kisa ta Ebola zuwa gida domin yi ma sa magani.

Ba'amirken mai suna Kent Brantly wanda likita ne, ya kamu da wannan cuta ne a kasar Liberia, ya yin da yake lura da masu dauke da ita, lamarin da ya sanya mahukuntan kasar sa, garzayawa da shi zuwa gida da nufin ceton rayuwar sa.

Bayanai daga Amurkan sun ce tuni aka kebe wannan likita a wani sashena musamman, dake asibitin jami'ar Emory dake birnin Atlanta, a yunkurin kare yaduwar cutar ta Ebola.

Kaza lika nan da 'yan kwanaki kadan, ake sa ran ita ma Nancy Writebol, da aka tabbatar ta kamu da cutar, za a mai da ita Amurkan domin lura da lafiyar ta. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China