Hadarin kamuwa ga masu tafiya zuwa kasashen yammacin Afrika da cutar ta fi kamari wato Guinee, Liberiya da Saliyo bai taka kara ya karya ba, duk da cewa ma idan wannan ziyara ta shafi yankunan da aka fara gano wannan cuta, in ji hukumar kasar Afrika ta Kudu game da cututtuka masu yaduwa (NICD).
Kamuwar cutar Ebola na bukatar wata cudanya ta jini, ban haya, sassan jiki ko kuma wasu ruwan jikin mutanen da suka kamu ko suka mutu da wannan cuta, ko dabobi, in ji hukumar NICD a cikin wata sanarwa. (Maman Ada)