Haka kuma za su bunkasa wani tsarin da zai shafi shiyyarsu baki daya da kuma bullo da wata hanyar dakatar da yaduwar wannan cuta, a cewar sanarwar hadin gwiwa da ta biyo karshen taronsu.
Darektar kungiyar kiwon lafiya ta duniya, madam Margaret Chan, da ta halarci wannan taro, ta jaddada cewa ya zama wajibi a dauki nagartattun matakai domin dakatar da yaduwar cutar Ebola a cikin sauran kasashen Afrika da ma duniya baki daya, ganin cewa kashi 70 cikin 100 na yaduwar wannan cuta na da nasaba da kai da kawo mutane a kan iyakoki ko kuma ta yin cudanya tsakanin al'ummomi. (Maman Ada)