A cewar wannan shiri, daruruwan kwararru za su isa a cikin kasashen da wannan cuta ta shafa domin taimakawa asibitoci wajen kula da masu fama da wannan cuta ganin yadda aiki ya masu yawa.
Sabon shirin ya kunshi dabarun kawar da yaduwar cutar Ebola a cikin wadannan kasashen uku da kuma hana yaduwarta zuwa sauran kasashe makwabtansu.
Tun cikin watan Maris din shekarar 2014, kimanin mutane 1323 aka tabbatar suna dauke da cutar, kana mutane 729 suka mutu a kasashen Guinee, Libieriya da Sierra Leone. Haka kuma ana zaton an gano wani mutum guda a Najeriya dake dauke da wannan cuta. (Maman Ada)