Wakilan da za su halarci taron Amurka da Afrika za'a yi musu gwaji kan cutar Ebola, in ji Obama
Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya bayyana a ranar Jumma'a cewa, dukkan wakilan Afrika da za su halarci dandalin Afrika da Amurka karo na farko da za'a bude a mako mai zuwa a birnin Washington za'a masu gwaji domin tabbatar da cewa ba su dauke da cutar Ebola. Matsalar Ebola, matsala ce da muke dauka da muhimmanci, in ji mista Obama, domin cewarsa matakan rigakafi ne da ake dauka ga wadanda za su halarci wannan dandali ta yadda za'a kaucewa duk wata barazana ta cutar Ebola.
Haka kuma Obama ya jaddada cewa wannan annoba ita ce mafi kawo barazana, kuma matakan da Amurka take aiwatar sun dace da halin da ake ciki game da wannan cuta.
Kafofin yada labaru na Amurka sun rawaito cewa shugabannin kasashen Liberiya da Sierra Leone, kasashen biyu da cutar tafi kamari sun soke ziyararsu zuwa Washington. (Maman Ada)