Yayin da tattalin arzikin kasar Zimbabwe ke samun farfadowa a shekarun baya, yana ci gaba da fuskantar wasu matsaloli, musamman ma rashin isashen kudi a kasuwa bayan da ta yi watsi da kudin kanta sa'an nan ta fara amfani da dalar Amurka. A cikin jawabinsa, shugaba Mugabe ya jaddada cewa, gwamnatinsa na kokarin daukar matakai don daidaita wannan matsala, ta yadda za a kau da shingen da ya hana a ci gaba da raya masana'antun kasar.
Ban da haka kuma, dangane da takunkumin da kasashen yammacin duniya suke ci gaba da saka ma kasar Zimbabwe, shugaba Mugabe ya soki kungiyar kasashen Turai, inda ya ce kungiyar na son ci gaba da kin amincewa da gwamnatin dake karkashin jagorancin Zanu-PF. Duk da cewa an yi babban zabe bisa doka, amma kungiyar EU ta ce wai an aikata magudi a wajen zaben.(Bello Wang)