A watan Fabrairu na shekarar bana, an ci gaba da samun ruwan sama kamar da bakin kwarya a lardin Masvingo dake kudancin kasar Zimbabwe, wadanda suka yi sanadiyar ballewar madatsun ruwa lamarin da ya haddasa ambaliyar ruwa a yankin, bugu da kari, ruwan ya rushe gidajen jama'a kimanin dubu 20, abin da ya sa aka tsugunar da su a wuraren dake da nisan kilomita 150 daga gidajensu. Kuma kasar Zimbabwe ta riga ta gabatar da kokon baranta na neman taimakon kudin dallar Amurka miliyan 20 ga gamayyar kasa da kasa don ya yi amfani da su a fannonin kula da jama'ar da ke fama da bala'in da sake gina gidaje.
Kuma kasar Sin ita ce kasa ta farko cikin kasashen duniya wadda ta ba da taimakon kudi ga kasar ta Zimbabwe.
Ministan kula da harkokin kananan hukumomin Zimbabwe Ignatius Chombo ne ya karbi taimakon kudin da kasar Sin ta ba baiwa kasar a madadin gwamnatin Zimbabwe, ya bayyana cewa, akwai dadadden zumuncin tsakanin kasar Sin da Zimbabwe, a lokacin da kasar Zimbabwe ke kokarin neman 'yancin kanta, kasar Sin ta ba da taimako da dama ga kasar, a halin yanzu kuma, kasar Sin ta sake ba da taimako mai muhimmanci ga kasar wajen fuskantar bala'in ambaliyar ruwa, babu shakka, taimakon kudin da gwamnatin kasar Sin ta samar ga kasarsa zai taimaka sosai ga jama'ar kasar Zimbabwe dake fama da bala'in. (Maryam)