A wannan rana kuma, ofishin labarai na fadar shugaban kasar Rasha ya ba da wata sanarwa, inda ya nuna cewa, shugabannin kasashen biyu sun tattauna kan rikicin kasar Ukraine. Duk da bambancin ra'ayi kan wasu batutuwa, amma bangarorin biyu sun jaddada cewa, ya kamata a kawo karshen rikicin kudancin kasar Ukraine ba tare da bata lokaci ba, sa'an nan a fara yunkurin shawarwarin siyasa domin warware batun. Bugu da kari, shugabannin biyu kuma sun nuna yabo ga shawarwarin da bangarorin uku da suka hada da tsohon shugaban kasar Ukraine, jakadan kasar Rasha dake Ukraine da kuma wakilan kungiyar tsaro da hadin gwiwa ta Turai suka yi dangane da yanayin kudancin kasar Ukraine a babban birnin kasar Belarus, Minsk. Shugabannin biyu sun kuma sa kaimi wajen ci gaba da irin wadannan shawarwari. (Maryam)