in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rasha ta yi gargadin mayar da martani game da sabbin takunkumin da aka kakaba mata
2014-07-17 20:35:17 cri
Kasar Rasha ta bayyana cewa, a shirye take ta mayar da martani bayan da kasar Amurka da kungiyar tarayyar Turai EU suka ba da sanarwar kara saka mata sabbin takunkumi.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta bayyana cikin wata sanarwa cewa, Rasha ba za ta yarda da duk wani kokari na shafa mata kashin kaji ba kuma tana da ikon daukar matakan da suka dace na mayar da martani.

Sanarwar ta ce, takunkuman da baitun malin Amurka ya sanya wa wasu 'yan kasar da manyan hukumomin kudi, makamashi da makaman kasar, da nufin daukar fansa game da abubuwan da ke faruwa a Ukraine batu ne da bai shafi Washington ba.

Shugaba Vladimir Putin na Rasha wanda yanzu haka ke Brazil ya bayyana cewa, takunkumin da aka sanya wa kasarsa, tamkar kaikayi ne zai koma kan mashekiya kuma zai raunata dangantakar da ke tsakanin Amurka da Rasha. Amma ya ce, har yanzu kofar tattaunawar Rasha a bude ta ke. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China