in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Rasha ya tattauna da takwarorinsa game da binciken hadarin jirgin saman MH17
2014-07-21 10:59:37 cri

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya zanta ta wayar tarho da takwarorinsa na kasashen Birtaniya, da Austrilia, da Holland da kuma Jamus, inda ya bayyana aniyar kasarsa game da samar da tallafin da ya wajaba, domin aikin bin habasin hadarin jirgin saman kasar Malaysian nan mai lamba MH17.

Shugaba Putin wanda ya zanta da shuwagabannin kasashen 4 da jiya Lahadi ya kuma jaddada cewa, kamata ya yi a kauracewa fidda duk wata sanarwa a siyasance, gabanin kammalar aikin binciken da ake yi.

Wasu bayanai daga shafin yanar gizon shugaban kasar Rashan sun nuna cewa, a tattaunawarsa da firaministan kasar Birtaniya David Cameron, Putin ya furta cewa, kasarsa na fatan ganin kungiyar jiragen saman fasinjoji ta kasa da kasa ta sa hannu a aikin bin bahasin hadarin jirgin saman na MH17, kana Rasha za ta ci gaba da samar da dukkanin taimakon da ya wajaba a wannan fanni.

Yayin da yake magana da shugabar gwamnatin kasar Jamus Madam Angela Merkel kuwa, shugabannin biyu sun amince da cewa, sakamakon tsanantar halin da ake ciki game da wannan hadari, abin da ya fi muhimmanci shi ne, dukkanin bangarorin da ke adawa da juna a kasar Ukraine, su ba da kariya ga lafiyar kwararrun dake bincike domin su gudanar da aikinsu cikin adalci.

Wata sabuwa kuma, an ce, dakarun da ke gabashin kasar Ukraine sun fidda wani jawabi kan shafinsu na Twitter, suna masu cewa an gano akwatin nadar bayanan jirgin saman na MH17, an kuma kai shi jihar Donetsk.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China