Zaunannen wakilin kasar Sin da ke MDD Mista Liu Jieyi ya bayyana a ranar 22 ga wata cewa, kasar Sin ta kalubalanci bangarorin Isra'ila da Palesdinu da su yi na'am da kokarin da kasashen duniya suke yi na neman zaman lafiya, su tsagaita bude wuta nan da nan ba tare da sharadi ba.
A wannan rana, an yi shawarwari a kwamitin sulhu na MDD, inda Liu ya ce, ya kamata bangarorin Palesdinu da Isra'ila su daina daukan ko wane irin matakan da za su kai a haddasa tashe-tashen hankula a tsakaninsu, don maido da kwanciyar hankali. Kasar Sin ta yi kira ga kasashen duniya da su kara aikin ceto na jin kai, da sa kaimi ga bangarorin da abin ya shafa da su bude tashoshin iyaka a zirin Gaza, domin ba da taimako, da sassauta hadarin jin kai a zirin Gaza.
Liu ya ci gaba da cewa, har kullum kasar Sin tana ganin cewa, ta hanyar yin shawarwari ne Isra'ila da Palesdinu za su yi zaman jituwa da juna, wannan dai ta zama hanya daya kawai da ta dace wajen daidaita matsalar Palesdinu, kuma hanya dai ta dace da babbar moriyar bangarorin biyu.
Bisa wani labari daban da muka samu, an ce, manzon musamman na kasar Sin kan harkokin Gabas ta Tsakiya Mista Wu Sike ya bayyana a ranar 22 ga wata a birnin Alkahira cewa, kasar Sin ta yi suka kan dukkan ayyuka kisa kan jama'a, ta kalubalanci Isra'ila da ta daina amfani da karfin soja, a sa'i daya kuma Sin tana fatan kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta Hamas ta daina harba rokoki. Kasar Sin ta nuna goyon baya ga ko wane irin kokarin da ake yi wajen tsagaita bude wuta ciki har da shawarar da Masar ta gabatar ba da dadewa ba kan tsagaita bude wuta a tsakanin Palesdinu da Isra'ila. (Danladi)