Yau Jumma'a 27 ga wata ne, aka bude taron tsaron kan iyaka da yankin teku na Sin karo na biyar a nan birnin Beijing, inda shugaban Sin Xi Jinping ya gana da wakilan da ke halartar taron, tare da jaddada cewa, tsaron kan iyaka da yankin teku na da muhimmanci kwarai,domin yana da alaka da tsaro da bunkasuwar kasar baki daya. A sabili da haka, dole ne ma'aikatan da wannan aiki ya shafa su kara fahimtar muhimmancinsa, su nuna jaruntaka tare da daukar nauyin da ke kansu, domin kafa wani tsarin tsaron kan iyaka da yankin teku na Sin mai karfi na zamani.
Bayan haka,shugaba Xi ya jaddada cewa, kamata ya yi a ba da fifiko ga batun ikon mallakar yankuna da tsaron kasa, da kara kyautata kulawa kan iyakar kasa da tabbatar da ikon kasa a yankin teku, domin a kiyaye su yadda ya kamata.(Fatima)