An ce, a ranar 9 ga wata, shugaba Obama zai tattauna da 'yan jarida na wasu manyan gidajen talabijin na kasar, inda zai bayyana muhimmancin daukar matakan soja kan Syria don hukunta gwamnatin kasar da aka zargin ta yi amfani da makamai masu guba, zai kuma yi alkawarin kayyade tsawon lokacin daukar matakan soja. Sai kuma a ranar 10 ga wata, Obama zai yi wani jawabi ga al'ummar kasar baki daya ta gidan talabijin, inda zai sake jaddada muhimmancin daukar matakan soja kan Syria da kuma ma'anarsa ta bangaren kiyaye moriyar Amurka, don sassauta damuwar jama'ar kasar da ke kin yarda da yakin.
A sa'i daya, a ranar 7 ga wata, sakataren harkokin waje na kasar Amurka, John Kerry ya isa Faransa, inda ya samu goyon baya daga gwamnatin kasar, sai dai a cewar gwamnatin Faransa, za ta jira har zuwa lokacin da masanan MDD kan makamai masu guba suka fitar da rahoton bincikensu, kuma ta fi son warware matsalar Syria ta hanyar siyasa.
Har ila yau, shugabar gwamnatin kasar Jamus, Angela Merkel ta bayyana a ranar 8 ga wata, inda ta ce, Jamus tana kokarin ganin kwamitin sulhun MDD ya dauki matakai na bai daya. Ta jaddada cewa, dole ne a daidaita matsalar Syria a siyasance, kuma Jamus ba za ta shiga aikin soja da ake son aiwatarwa ba.(Lubabatu)