in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta kara kasafin kudinta na tsaro a shekarar 2014
2014-03-06 12:47:35 cri

Kasar Sin tana shirin kara kashi 12.2 cikin 100 a kasafin kudinta na tsaro a shekarar 2014, wato Yuan biliyan 808.2, kwatankwacin dala biliyan 132.

Wannan bayani yana kunshe ne cikin daftarin rahoton kasafin kudin da aka gabatar wa majalisar wakilan jama'ar kasar ranar Laraba domin ta yi nazari a kai, adadi mafi yawa da kasar Sin ta ware a harkokinta na tsaro tun shekara ta 2011.

A cewar Sun Huangtian, mataimakin shugaban sashen tsare-tsaare na rundunar sojojin 'yantar da al'umma ta kasar Sin (PLA), za a yi amfani da kudaden ne wajen samar da kayayyakin aiki na zamani, inganta yanayin aiki da rayuwar sojojin, tare da inganta tsarin tafiyar da aikinsu, ta yadda zai dace da zamani.

Wani manazarci a cibiyar kimiyyar soja, kana wakili a majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Chen Zhou, ya ce, kudaden da kasar Sin take kashewa a harkokinta na soja ba su taka kara sun karya ba, idan aka kwatanta da sauran manyan kasashen duniya.

Ya kara da cewa, muddin kasar Sin tana son kare kasarta tare da samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a shiyyar, da ma duniya baki daya, wajibi ne ta karfafa matakanta na tsaro. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China