in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashe da dama sun yi atisayen soja cikin hadin gwiwa a birnin Qingdao na kasar Sin
2014-04-23 16:17:48 cri

Kasashe 8 sun gudanar da atisayen soja cikin hadin gwiwa dake mai da hankali kan aikin ceto, aikin da ya kunshi jiragen ruwan yaki 19, da jiragen sama masu saukar ungulu 7.

Sojojin kasashen da suka shiga wannan atisaye sun hada da na kasashen Sin, da Pakistan, da Indonesiya, da Singapore, da Indiya, da Malyasia, da Bangladash da kuma Brunei.

Sojojin ruwan kasar Sin sun gudanar da atisayen soja bisa taron shekara-shekara na dandalin sojin yammacin tekun Pacific, domin ganin yadda sauran kasashe ke aiwatar da makamancin wannan aiki, da zummar kara fahimtar juna, da cimma matsaya daya, da amincewa da juna.

Kaza lika sojojin Sin na fatan amfani da wannan dama, wajen sada zumunta tsakanin wadannan kasashe, da tattauna yadda za a aiwatar da aikin ceto a kan teku, tare kuma da sa kaimi ga hadin kai tsakanin sojojin tekun wadannan kasashe, kan kiyaye tsaron sararin teku, ta yadda za a bunkasa kwarewa mai nagarta wajen tinkarar halin ko ta kwana a kan teku. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China