A ranar 25 ga wata, manyan jagororin atisayen sojin ruwa na shekarar 2014 na hadin gwiwar Sin da Rasha sun zanta da manema labaru cikin hadin gwiwa, inda babban mai jagoranci na bangaren Sin, kuma mataimakin kwamandan sojojin teku na kasar Sin laftana-janar Tian Zhong ya yi nuni da cewa, idan aka kwatanta wannan atisayen soja da sauran sau biyu da aka gudanar a da, ana iya ganin cewa, an cimma matsaya game da fannoni hudu a wannan karo, wato akwai batun gudanar da atisayen soja bisa manyan tsare-tsare, da ya shafi dukkan fannoni, ciki hadda bangarori daba daban da suka shafi hakikanin halin da ake ciki.
Mista Tian yana ganin cewa, a wannan karo, an yi gwaje-gwaje kan ba da jagoranci na hadin kai da ba da tabbaci yayin da sojojin Sin da Rasha suke daukar matakai tare a kan teku. Hakan dai ya inganta kwarewar sojojin ruwa na kasashen biyu wajen tinkarar barazana daga aikin tsaro a kan teku, kuma sojojin da suka halarci atisayen soja sun kara kwarewarsu, an kuma cimma burin da aka tsara a baya, sabo da haka, an karfafa dangantakar abokantaka da hadin kai bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni tsakanin kasashen biyu, da kuma nuna niyya da kwarewarsu wajen kiyaye zaman lafiya a shiyyarsu.
A nasa bangare, mataimakin kwamandan sojojin teku na kasar Rasha laftana-janar Alexander Fedotenkov ya bayyana cewa, yayin da ake atisayen soja, sojojin ruwa na kasashen biyu sun yi koyi da juna, sun gama aiki tare, inda suka karfafa niyya da kwarewarsu wajen daukar matakan soja cikin hadin gwiwa. Rasha da Sin dukkansu sun kasance manyan kasashe da ke dab da tekuna, Don haka kuma ya kamata sojojin ruwansu su ba da tabbaci ga zaman lafiyar yankin Asiya da tekun Pacific. Ya kuma kamata bangarorin biyu su ci gaba da hadin kai da raya dangantakar abokantaka a tsakaninsu. (Danladi)