A cewar kungiyar NRC, wata kungiya mai zaman kanta dake aiki tare da kungiyar kula da 'yan gudun hijira ta MDD, ma'aikatan biyu sun dawo da kammala aikinsu na rarraba wasu kayyakin bukatun yau da kullum ga 'yan gudun hijira da suka shiga baya bayan nan cikin wannan yanki.
A cikin wannan sanarwa, babban jami'in dake kula da ayyukan jin kai a kasar Mali, David Gressly yayi allawadai da wadanda suka haddasa mutuwar wadannan ma'aikatan biyu.
Akwai bacin rai matuka, ma'aikatan jin kai su mutu a yayin da suke kokarin kai taimako ga mutanen dake cikin mawuyacin hali. Ina kira ga dukkan bangarorin da wannan rikicin kasar Mali ya shafa dake arewacin kasar dasu kiyaye tsaron lafiyar fararen hula da kuma bada dama ga kungiyoyin agaji don su kai taimako ga mutane in ji mista Gressly.
A cewar wannan sanarwa, kusan kungiyoyin bada agaji dari ne na kasar Mali dana kasashen waje suke wannan kasa dake yammacin Afrika inda suke kai taimakon ruwan sha, abinci, bada jinya da matsugunni ga miliyoyin mutanen kasar Mali. (Maman Ada)