Kakakin ma'aikatar kungiyar tarayyar Turai game da harkokin waje (SEAE) ya yi maraba da matsayin Aljeriya a wannan fanni, tare da taimakon kungiyar ECOWAS, tarayyar Afrika AU, MDD, EU da kuma kungiyar kasashen musulmi ta OCI, tare da taimakon kasar Burkina Faso, Mauritaniya, Nijar da Chadi dake halartar wadannan shawarwari na manyan jami'ai.
Haka kuma kakakin ya jaddada goyon bayan kungiyar Turai da ci gaban wannan zaman tebur, domin cimma hanyoyi masu nagarta na aiwatar da niyyar dukkan bangorin da abin ya shafa ga taimakawa zaman lafiya da sansanta 'yan kasar Mali ciikin karko. (Maman Ada)