Kungiyar MNLA, kwamitin hadin kan yakin Azawad na HCUC da kuma 'yan tawayen Larabawa na yankin Azawad (MAA) sun cimma rattaba hannu a kanta a daren jiya, in ji tawagar MDD dake kasar.
Wannan sanarwa ta biyo bayan tattaunawar shiga tsakani a karkashin jagorancin shugaban kasar Mauritaniya Mohamed Ould Abdel Aziz dake kuma shugaban tarayyar Afrika a wannan karo.
Sake barkewar rikici na baya bayan nan a arewacin kasar Mali ya janyo kara barazanar kara tura wannan kasa dake yammacin Afrika cikin tashin hankali da zaman dar dar wanda kuma ba ta jima da samun zaman lafiya ba. (Maman Ada)