in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta goyi bayan tsawaita wa'adin tawagar MDD a Mali
2014-06-26 17:05:24 cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin madam Hua Chunying, ta bayyana gamsuwar kasar Sin game da tsawaita wa'adin aikin tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a Mali, a kokarin da ake yi na ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.

Madam Hua ta furta hakan ne a Alhamis din nan, ta na mai cewa daga watan Afrilun bara zuwa yanzu, tawagar MDDr dake Mali ta gudanar da ayyukanta cikin yakini, bisa shawarar da kwamitin sulhu na MDD ya yanke, ta kuma taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Mali.

A cewar ta yanzu haka ana ci gaba da fuskantar matsalar tsaro a Mali, don haka Sin ke goyon bayan tsawaita wa'adin aikin tawagar MDDr, domin cimma burin da aka sanya gaba, ciki hadda batun tallafawa yunkurin kyautata yanayin siyasa da tabbatar da daidaito tsakanin al'ummun kasar.

Dadin dadawa, madam Hua ta ce a matsayin zaunanniyar mamba ta kwamitin sulhun MDD, Sin tana bada himma ga daidaita batutuwan da suka fi jawo hankali a shiyya-shiyya cikin lumana, tare da halartar ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD cikin yakini. Baya ga nuna goyon baya da take yi ga tabbatar da zaman lafiya, da kwanciyar hankali a nahiyar Afirka.

Bugu da kari kasar Sin ta tura tawaga mai kunshe da jami'ai 395, domin aiki cikin tawagar MDD dake kokarin tabbatar da zaman lafiya a Mali, tawagar dake kunshe da sojoji 170, da sojoji injiniyoyi 155, da kuma jami'an kula da lafiya 70.

Tuni kuma dukkansu suka kammala aikinsu yadda ya kamata, tare da samun amincewa da yabo daga MDD da gwamnatin kasar Mali.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China