A ranar 21 ga wata ne, babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya yi kira ga Palesdinu da Isra'ila da su tsagaita bude wuta nan da nan, tare da yin shawarwari da juna.
Ban Ki-moon ya bayyana a gun taron manema labaru da ya shirya tare da ministan harkokin wajen Masar Sameh Shoukry cewa, rikicin da Palesdinu da Isra'ila suka shafe makonni biyu suna yinsa, ya haddasa mutuwa da jikata fararen hula, lamarin ne da ba za a amince da shi ba, tilas ne bangarori daban daban da abin ya shafa sun dauki matakai don dakatar da aikin nuna karfin tuwo, da ba da taimako ga aikin ceto na jin kai.
Ban Ki-moon ya nuna godiya ga Masar da ta gabatar da shawarar tsagaita bude wuta, da bude iyakarta da ke Rafah a cikin gajeren lokaci domin ba da jinya ga wadanda suka ji rauni, da ta ba da taimakon abinci da magunguna ga zirin Gaza, a cewarsa, Masar tana taka wata muhimmiyar rawa wajen samun sulhuntawa dangane da rikicin Palesdinu da Isra'ila.
A nasa bangaren, Shoukry ya ce, Masar za ta kara bayar da taimako wajen maido da zaman lafiya da kare 'yanci da moriyar Palesdinawa.
Kafin haka kuma, Ban Ki-moon ya kai ziyara kasashen Kuwait, da Qatar, kana bayan ziayararsa a Masar, zai kuma ziyarci Jordan, da Isra'ila da Palesdinu, inda zai yi shawarwari da bangarorin domin sa kaimi ga tsagaita bude wuta tsakanin Palesdinu da Isra'ila. (Danladi)