An ce, masana'antun injuna na kasar Sin sun fara samun farfadowa a shekarar 2013. Yayin da kasar Sin ke kokarin cimma burinta na kasancewa wata kasa mai karfi wajen kera injuna, ta fara dogaro bisa hanyar kyautatuwar ingancin kayayyki da ba da ayyukan hidima na kirkire wajen neman samun ci gaba, a maimakon dogaro bisa hanyar kara yawan kayayyaki kawai. Hakan ana sa ran ganin ci gaba da kiyaye karuwar yawan kudin da aka samu daga masana'antun injuna har zarce kashi 10 cikin dari a bana, yayin jimillar ta karu da kashi 8 cikin dari a fannin fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje.
Hakazalika kuma, akwai wasu matsaloli kan wannan sana'a a watanni biyar na farkon bana. Wani jami'in kungiyar hadin gwiwa ta masana'antun injuna ta kasar Sin ya nuna cewa, idan ana son kawar da matsalolin, tilas ne a yi watsi da tsarin dogara a kan fadada ayyuka a kasashen waje da kuma rage farashin kayayyaki don neman samun moriya. (Zainab)