in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cigaban masana'antu ya ragu a Afrika ta Kudu
2014-06-11 10:14:37 cri

Adadin kayayyakin da masana'antu suke sarrafawa a kasar Afrika ta Kudu ya ragu da kashi 1,8 cikin 100 a tsawon watanni uku da aka rufe a cikin watan Afrilun shekarar 2014, idan aka kwatanta da watanni ukun da suka gabata, in ji wasu alkaluman da aka fitar a ranar Talata. Shida daga cikin masana'antu goma a kasar sun samu adadin bunkasuwa da ya ragu a cikin wannan lokaci, a cewar hukumar kididdiga ta kasar Afrika ta Kudu.

Abubuwan da suka taimaka ga wannan ja da baya na kashi 1,8 sun fito daga bangaren man fetur, sinadari, roba, motoci da ma karafunan motoci da makamantansu da kuma kayayyakin sufuri.

Wannan rahoto zai dan janyo shakku ga amincewar masu zuba jari a yayin da kuma GDP din kasar ya fado zuwa kashi 0,6 cikin 100 a farkon watanni uku na wannan shekara, wanda ya kasance ja da baya karo na farko tun bayan rikicin hada-hadar kudi na duniya a shekarar 2009. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China