Wani sabon rahoton tattalin arzikin Afirka da hukumar kungiyar AU ta fitar a jiya Talata, ya nuna aniyar da ake da ita, game da daukar matakan bunkasa masana'antu domin fadada arzikin nahiyar Afirka.
Rahoton wanda aka fitar yayin wani taro da ya gudana a jami'ar birnin Pretoria mai taken "Kyawawan tsare-tsaren bunkasa masana'antu, inganta cibiyoyin bincike da samar da managartan shirye-shirye", ya kunshi sakamakon bincike da aka yi kan kasashe 11, game da tasirin ababen da ke iya bunkasa arzikin nahiyar ta Afirka.
Kaza lika rahoton ya bayyana bukatar da ake da ita ga kasashen Afirka, da su dauki matakan samar da manufofin bunkasa masana'antu, wadanda za su kai ga cimma nasarar daga matsayin masana'antun su zuwa matsayi na gaba.
Hakan dai ya zo daidai gabar da wasu manazarta ke kallon Afirka a matsayin alkiblar ci gaban tattalin arzikin duniya. (Saminu)