Shugaban a cikin sanarwar ya ce, ya kamata dukkanin masu zabe su yi kokarin kada kuri'arsu yayin zaben, su nuna goyon bayansu ga dan takarar da suka amince da shi. Ya kara da cewa, yadda masu zabe suka nuna himmarsu wajen kada kuri'ar shi ne zai kasance martanin da suka mayar ga wadanda suka lalata moriyar kasar, haka kuma ga wadanda ke nuna shakku kan ko al'ummar kasar suke da sanin ya kamata ta bangaren siyasa da kuma ko suna da karfin kiyaye kwanciyar hankali da tsaro a kasar ko a'a.
Za a gudanar da zaben shugaban kasar ta Aljeriya ne a ranar 17 ga watan Afril mai zuwa, kuma kawo yanzu, mutane sama da 130, ciki har da shugaban mai ci yanzu Abdelaziz Bouteflika ne, suka bayyana aniyarsu ta tsayawa takara a zaben.(Lubabatu)