Sanarwar da ta fito daga ofishin shugaban kasar ta ce Shugaba Bouteflika ya kuma nada Ahmed Ouyahia a matsayin Ministan kasa kuma Shugaban ma'aikata na ofishin Shugaban kasar wanda ya maye gurbin Mohammed Moulay Guendil wanda aka ba shi wani aiki daban.
Shi kuma Abdelaziz Belkhadem aka nada shi Ministan kasa kuma mai baiwa Shugaban kasa shawara na musamman, in ji sanarwar.
Mr. Ouyahia da Mr. Belkhadem dukkanninsu tsoffin firaministoci ne kuma tsoffin shugabannin jami'iyun dake mulkin kasar wato National Democratic Rally ko (RND) da kuma Liberation Front (FLN). (Fatimah)