Rahoton ya nuna cewa, aikin zai shafi iyalan manoma dubu 100, a ciki, iyalai sama da dubu 30 suna aikin kiwon dabbobi wanda mata sun fi kwarewa. Daga bisani kuma, za a ba da horaswa ga manoma fiye da dubu dari 5, tare da ba da jagoranci ga masu fama da talauci sama da dubu dari 8 domin samun aikin yi, a fannonin da suka shafi kiwon dabbobi, da sayar da hajoji da dai sauransu.
Har ila yau, shirin zai kuma ba da taimako wajen kafa cibiyoyin ba da tallafi kan ayyukan kiwon dabbobi guda 177, da cibiyoyin tattara da kuma gyaran madara guda 3, kasuwannin sayar da dabbobi guda 2, da kamfanonin yanka dabbobi guda 8, dakunan gwaje-gwaje na likitocin dabbobi guda 7, da kuma tashoshin binciken cututtukan dabbobi masu yaduwa sama da 10 a kasar. (Maryam)