Ministan harkokin waje da na 'yan kaka gida a ketare na kasar Jordan Nasser Joudeh ya gana da manzon musamman na kasar Sin kan batutuwan Gabas ta Tsakiya Mista Wu Sike a ranar 20 ga wata a birnin Amman, inda bangarorin biyu suka yi musanyar ra'ayoyi kan halin da ake ciki tsakanin Palesdinu da Isra'ila.
Wu ya ce, Isra'ila da Palesdinu sun kara tashe-tashen hankula a tsakaninsu, kasar Sin tana mai da hankali sosai kan haka tare da nuna damuwarta. Kasar Sin ta soki ko wane irin farmakin da aka kai wa fararen hula, ta kuma yi maraba da shawarar tsagaita bude wuta da Masar ta gabatar, haka kuma kasar Sin ta kalubalanci bangarori daban daban da abin ya shafa da su mayar da tsaron jama'a da zaman karko a shiyyar a gaban kome, su mayar da martani cikin yakini ga shawarwari da kasashen duniya suka gabatar da kuma kokarin da suke yi wajen tsagaita bude wuta, domin su daina rikici da juna nan da nan, kana su guji daukar matakan da ke iya haddasa tashe-tashen hankula a tsakaninsu.
Joudeh ya yi nuni da cewa, Jordan tana maraba da kasar Sin ta kara taka wata muhimmiyar rawa a kan batun Palesdinu, tana son kara cudanya da hadin kai da kasar Sin bisa bangarori biyu ko fiye, don yin kokari tare wajen sa kaimi ga tsagaita bude wuta tun da wuri a tsakanin Palesdinu da Isra'ila tare da maido da shawarwari a tsakaninsu, ta yadda za a sa kaimi ga warware matsalolin Palesdinu nan da nan kuma cikin adalci. (Danladi)