in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Sin ya gana da takwaransa na Girka
2014-06-20 20:39:08 cri
A jiya da yamma ne firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gana da takwaran aikinsa na kasar Girka Antonis Samaras a birnin Athens, inda suka tattauna kan hanyoyin inganta dangantaka da hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata, tare da cimma matsayi daya kan wasu batutuwa.

Bayan tattaunawar, firaministocin kasashen biyu sun halarci bikin kulla yarjejeniyoyin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu kan fannonin al'adu, tattalin arziki, cinikayya, zuba jari, ayyukan dake shafar harkokin teku, yin rigakafin bala'u, samar da kayayyakin more rayuwa da dai sauransu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China