Shugaban cibiyar nazarin tattalin arziki da siyasa ta Turai, kuma tsohon manazarci mai kula da harkokin tattalin arziki na kasar Fredrik Erixon ya bayyana cewa, ziyarar Li Keqiang za ta kara karfafa hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Ingila da Sin, kana ta aza tubalin samun moriyar juna yayin da ake kara inganta dangantakar hadin gwiwa a tsakanin Sin da EU a fannonin ciniki da tattalin arziki.
Jaridar European Times ta kasar Faransa ta rubuta wani sharhi a ranar 18 ga wata, inda ta ce, ziyarar da firaminista Li ya kai a kasashen Turai ta nuna alamar samun bunkasuwa cikin lumana da samun moriyar juna ga nahiyar Turai. Kana kasar Sin ta nuna goyon baya da bada gudummawa ga kasashen Turai masu fama da rikicin bashi ke addabarsu, wannan ya bayyana cewa, kasar Sin abokiya ce ta kasashen Turai.
Ban da wannan kuma, kamfanonin dillancin labaru na AP, Reuters, AFP, BBC sun bayar da rahotanni game da ziyarar Li Keqiang a kasar Ingila, a ganinsu, ziyarar za ta taimaka wajen inganta hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu a fannonin tattalin arziki da cinikayya, kana ta bayyana karuwar tasirin da Sin ke kawo wa nahiyar Turai. (Zainab)