Babban jami'in hukumar 'yan sandan jihar Kano ya bayyana wa 'yan jarida a wurin da bam din ya tashi cewa, an riga an damke wanda ake zargi da dasa shi, kuma a yanzu haka ana ci gaba da bincike kan lamarin kafin gabatar da karin bayani ga kafofin watsa labaru.
Bisa bayanan da mahukuntan kasar suka bayar, an ce ya zuwa yanzu, yawan mutanen da suka mutu a sakamakon lamarin ya kai 8. Koda yake wasu shaidu da suka ganewa idanun su aukuwar lamarin sun ce, yawan wadanda suka rasu ya kai akalla mutum 18.
Ya zuwa yanzu dai, babu wata kungiya ko wani mutum da ya dauki alhakin kai wannan hari, koda yake dai bangarori daban daban a kasar na zargin kungiyar Boko Haram wadda a baya ta sha kaddamar da makamantan wadannan hare-hare. (Zainab)