in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Boma-bomai sun tashi a birnin Lagos na Nijeriya
2014-06-27 15:48:06 cri
'Yan sandan Nijeriya sun tabbatar a daren ranar 26 ga wata cewa, an samu fashewar boma-bomai sau biyu a jere a yankin Apapa dake birnin Lagos, cibiyar tattalin arzikin tarayyar Nijeriya, wadanda suka haddasa mutuwa da raunatar wasu mutane, amma 'yan sandan ba su bayyana yawansu ba.

Kakakin 'yan sandan jihar Lagos ya bayyana cewa, an samu fashewar boma-bomai din cikin wani dakin ajiye mai da kuma kofarsa wanda ke yankin Apapa a daren ranar 25 ga wata. Yanzu 'yan sanda sun riga sun killace wurin da lamarin ya faru tare da jibge 'yan sanda domin kiyaye tsaro da fara bincike kan lamarin.

Ya zuwa yanzu, babu wata kungiyar da ta dauki alhakin kai hare haren. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China