in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kashe makiyaya 13 a jihar Taraba dake Nijeriya
2014-06-30 10:26:21 cri
'Yan sandan jihar Taraba dake arewa maso gabashin tarayyar Nijeriya sun bayyana cewa, makiyaya 13 ne suka rasa rayukansu sakamakon harin da wasu dakaru suka kai musu a ranar 28 ga wata.

Kakakin hukumar 'yan sandan jihar ta Taraba ya bayyanawa taron manema labaru cewa, makiyayan fulani su 13 sun rasu ne yayin da wasu mahara suka kai musu farmaki a kan wani karamin titi dake jihar.

Kakakin ya kara da cewa, kawo yanzu ba a san dalilin da ya haddasa aukuwar lamarin ba, sai dai 'yan sandan jihar suna kara sa ido a yankin da lamarin ya faru.

A hannu guda kuma wani jami'in gwamnatin jihar ya bayyana cewa, watalika an kai harin kan makiyayan ne a hanyarsu ta koma gida bayan sun sayar da wasu dabbobi nasu. Kana jami'in ya yi alkawari cewa, 'yan sanda za su kama maharani tare da gurfanar da su gaban kuliya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China